Mutuwar Mandela : Sepp Blatter na juyayi

Mandela da Blatter
Image caption Blatter ya yaba wa Mandela kan nasarar da aka samu ta gasar Kofin Duniya ta 2010 a Afrika ta Kudu.

Shugaban Hukumar Kawallon kafa ta duniya, Fifa, Sepp Blatter ya jagoranci ta'aziyya da yabon da ake yi wa abokinsa, shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko, Nelson Mandela wanda ya mutu yana shekara 95.

Mr Mandela ya yi amfani da harkokin wasanni wajen hada kan al'ummar kasarsa bayan mulki na tsananin wariyar launin fata.

Blatter ya ce: '' cikin tsananin juyayi ina ta'aziyyar mutumin da yake na daban.

'' Shi da ni mun yi imani da gagarumin tasirin da wasan kwallon kafa ke da shi wjen hada kan jama'a.''

Blatter ya kara da cewa: ''Watakila yana daya daga cikin wadanda suka fi kishin dan'adam a lokacinmu.''

Mr Mandela ya taba cewa: Wasa yana da karfin sauya duniya. Yana da karfin karfafa gwiwa, yana da karfin hada kan mutane ta hanyar da ba komai ne zai iya ba.''

Tsohon kaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa ta Afrika ta Kudu kuma tsohon dan wasan Everton Steven Pienaar mai shekaru 31 shi ma ya yi ta'aziyyar : ''cikin hawaye, Uban babban kasar nan ya rasu: Allah ya jikan TATA MADIBA.''

Karin bayani