Premier : Za a karrama Mandela a wasanni

kwallon kafa
Image caption Wasu 'yan wasan zari-ruga a Italiya kuwa za su daura bakin kyalle ne a hannuwansu domin karrama Mandela

Za a yi tafi na tsawon minti daya a wasannin Premier domin martaba tsohon shugaban Afrika ta Kudu, Nelson Mandela wanda ya mutu ranar Alhamis yana da shekara 95.

A yankin Scotland ma za a yi tafin a lokutan wasanni, haka kuma a yayin wasannin lig da na Kofin FA zagaye na biyu.

Kafin fara wasan kusa da na karshe na gasar kwallon zungure na tebur (snooker) ta Birtaniya a York yau Juma'a sai da aka yi tsit tsawon minti day domin karram Mandela.

'yan Afrika ta Kudu da shugabannin duniya n ci gaba da karram Nelson Mandela wand ya jagoranci sauyin mulki daga tsuraru farar fata.

Mr Mandela ya shafe shekaru 27 a kurkuku kafin ya zama shugabn kasar bakar fata na farko a 1994.