Marseille ta raba gari da koci Elie Baup

Elie Baup
Image caption Kocin ya taka rawar gani a kakar wasa ta bara

Kungiyar kwallon kafa ta Marseille dake Faransa ta sallami kocinta Elie Baup bayan da tayi rashin nasara a hannun Nantes da ci daya mai ban haushi ranar Juma'a

Kocin mai shekaru 58 ya jagoranci kungiyar kaiwa matsayi na biyu a teburin gasar Faransa da kuma kai kungiyar gasar cin kofin zakarun Turai a bara, amma a kakar bana kungiyar tana matsayi na shida a teburi.

Shugaban kungiyar Vincent Labrune ya ce kungiyar na karancin kwazo da fitattun 'yan wasa da aka yi tsammani a kakar bana.

An nada diraktan wasannin kungiyar Jose Anigo ya maye gurbinsa a wasanni hudu da za su kara a nan gaba har da karawar da za suyi a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba da Borussia Dortmund.