Moyes: Za mu iya lashe Kofi

David Moyes
Image caption Har yanzu kocin yana da yakinin United za ta iya lashe kofin bana

David Moyes ya ce kungiyarsa ta Manchester United har yanzu tana daga cikin kungiyoyin da za su iya lashe kofin Premier bana, duk da rashin nasara a wasanni biyu da kungiyar ta yi a gidanta a kwanaki hudu.

Arsenal da ke matsayi na daya a Teburin Premier ta baiwa United tazarar maki 12 kafin ta kara da Everton a yau.

Bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da ci daya mai ban haushi da kuma hannun Everton, Moyes ya ce "ina da karfin gwiwar za mu kai labari, ina fata muna daga cikin wadanda za mu lashe kofin a karshen kakar wasa."

Da aka tambaye shi me ya sa yake da karfin gwiwar lashe kofi sai ya ce" Saboda 'yan wasan da muke da su, kuma ina tare da zakarun kofi."

Ranar Asabar Newcastle ta samu nasarar farko a filin Old Trafford, rabonta da ta sami nasarar a filin tun shekaru 41 da suka wuce, kuma rashin nasara ta uku da United ta yi a gida a kakar wasan bana.