Premier: Arsenal da Everton 1-1

Arsenal Everton
Image caption Arsenal tana matsayi ta biyu a teburin Premier da tazarar maki biyar

Arsenal ta tashi wasa 1-1 a karawar da ta yi da Everton a gasar Premier wasan sati na 15.

Arsenal ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Mesut Ozil a daidai minti na 80 da take kwallo, kuma saura minti 6 a kammala wasa sai Everton ta zare kwallo ta hannun dan wasan da ya shigo canji Gerard Deulofeu wasa ya koma 1-1.

Mai tsaron ragar Everton Tim Howard ya sha dauki ba dadi tare da Aaron Ramsey da Olivier Giroud, shima Szczesny na Arsenal ya kade kwallon Mirallas da ta kusa fadawa raga.

Daf da za a tashi wasa Giroud ya buga kwallo ta doki tirke, haka aka tashi wasa Arsenal tana ja gaba a teburin Premier da tazarar maki 5 ga kungiyar Liverpool da take matsayi ta biyu.