Ballon d'Or: Messi da Ribery da Ronaldo

Messi, Ronaldo and Ribery
Image caption Messi, Ronaldo da Ribery

An fidda sunayen 'yan kwallon kafa uku da za a zabi daya a matsayin gwarzon dan kwallon duniya na bana.

'Yan wasa ukun da aka zabo sun hada da Lionel Messi na Argentina mai wasa a Barcelona da Franck Ribery na Faransa mai wasa Bayern Munich da kuma Cristiano Ronaldo na Portugal mai wasa a Real Madrid.

An zabo 'yan wasan uku ne daga cikin 'yan kwallo 25 da aka ware tun a watan Oktoba har da dan wasan da aka saya mafi tsada a bana Gareth Bale.

Ana sa ran bayyana gwarzon a ranar 13 ga watan Janairu a shekarar 2014 a Zurich.

Messi dake wasa a Barcelona shine ya lashe kyautar sau hudu a jere, amma a wannan shekarar ana hasashen dan wasan Real Madrid Ronaldo shine zai iya lashe kyautar bana.