Munich ta lashe wasanni 40 a jere

Bayern Unbeating
Image caption kocin ya ce yayi murna matuka da yake kocin Munich

Kocin Bayern Munich Pep Guardiola ya ce nasarar da kungiyarsa ke samu ba nasararsa shi kadai ba ce, nasar kungiyar ce gabaki daya.

Munich ta casa kungiyar Werder Bremen da ci 7-0 a ranar Asabar.

Kungiyar ta zakarun kofin Nahiyar Turai da kofin Jamus ta lashe wasannin 40 a jere a gasar Bundesliga, har da wasanni 15 da Guardiola ya lashe tun lokacin da ya koma kungiyar a farkon kakar wasan bana.

Kocin ya sanar ta shafin intanet na kungiyar cewa "ina godiya matuka ga 'yan wasana,saboda suna da kyau sosai. Kungiyar ce ta hada wadannan gwanayen 'yan wasa. Kuma daman ana ganin kyawun kociya ne idan 'yan wasansa suna da kyau saboda haka an girmama ni da bani wannan aiki.''