Madrid ta kasa casa Olimpic de Xativa

Carlo Ancelotti
Image caption Kocin ya ce kakar wasan bana Madrid na zura kwallaye

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce bai damu da wasan da suka tashi babu ci ba, a karawar da sukayi da Olimpic de Xativa a gasar kofin Copa del Rey a wasan zagaye na hudu.

A karawar an kori Cristiano Ronaldo a wasan, aka kuma cire Gareth Bale daga wasan sakamakon zazzabin Flu, kuma Madrid ba ta samu nasara a kan kungiyar da take matsayi na 9 a teburin gasar Segunda B, gasa ta uku kafin La-liga ta kasar Spain ba.

Kungiyar da Madrid ta kasa casa wa, an kafa ta a shekarar 1932 a Valencia, sai dai ta kwashe tsahon shekarun kafuwarta a gasa ta hudu a Spain kuma bata haura matakin da take a yanzu.

Anceloti ya ce" Kungiyarmu ba ta da matsalar rashin zura kwallaye a raga domin muna zura kwallaye, kuma ba a zura mana kwallaye da yawa, saboda haka komai yana tafiya yadda ya kamata."