BBC za ta nuna wasan Ingila da Italiya

Italy England
Image caption Jama'a da dama za su sami damar kallon wasan kofin duniya kai tsaye

BBC za ta nuna karawa tsakanin Ingila da Italiya ranar 14 ga watan Yuni a gasar kofin duniya bayan da aka sanar da raba izinin nuna wasannin kofin duniya a Brazil a shekarar badi.

BBC za ta fara nuna wasan Spain da Holland kai tsaye a ranar 13 ga watan Yuni.

Gidan talbijin na ITV zai nuna kafsawa a wasannin Ingila da Uruguay da Costa Rica da kuma wasan farko a karawa tsakanin Brazil da Croatia ranar 12 ga watan Yuni.

BBC za kuma ta nunu wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar da kuma wasannin kusa dana karshe, inda ITV za ta nuna wasannin kusa da kusa dana karshe, sai dai dukkansu za su nuna wasan karshe ran 13 ga watan Yuli.

Ingila bata taba casa Italiya a mahimmin wasa ba, sai dai bata taba karawa da Costa Rica ba.