UEFA: Galatasaray da Juventus

Galatasaray vs Juventus
Image caption Juventus na fatan samun nasara ta kai maakin wasan gaba

Yau ake cigaba da gasar cin kofin zakarun Turai a wasannin karshe na cikin rukunnai, da za a kara a wasanni 8 a filaye daban daban.

Galatasaray za ta karbi bakuncin Juventus a wasan 'yan rukuni na biyu, daya kunci Real Madrid da FC Kobenhavn.

Galatasaray nada maki uku ita kuwa Juventus na da maki shida, kuma dukkansu suna bukatar samun nasara a wasan da za su kara a yau.

Tuni Real Madrid ta samu kaiwa wasan gaba da maki 13 kuma za ta kara da FC Kobenhavn mai maki hudu a Denmark.

Sauran wasannin da za kara a sun hada da:

Manchester United vs FC Shakhtar Donetsk Real Sociedad vs Bayer 04 Leverkusen Bayern Munich vs Manchester City Olympiacos vs RSC Anderlecht Benfica vs Paris Saint-Germain FC Viktoria Plzen vs CSKA Moskva