Britaniya za ta yi taron hana sayar da wasa

DJ Campbell
Image caption DJ Campbell na cikin wadanda ake zargi da sai da wasa

Gwamnatin Britaniya ta gayyaci shugabannin hukumomin wasanni biyar domin tattauna zargin sayar da wasannin kwallon kafa.

Ministar al'adu Maria Miller ce za ta jagoranci ganawar da shugabannin kwallon kafa, kurket, tseren dawaki, da wasannin zari-ruga na rugby league da rugby union.

An dai kama mutane shida, ciki har da dan wasan Blackburn Rovers DJ Campbell bisa zargin sayar da wasa.

Ministar ta kira taron ne domin musayar ra'ayi kan matakan da za'a dauka wurin hana sayar da wasanni a Britaniya.