Man City ta takawa Bayern birki

Bayern vs City
Image caption Karon Bayern Munich da Manchester City

Manchester City ta kawo karshen wasanni 10 a jere da Bayern Munich ta yi ta na samun nasara a gasar zakarun Turai, amma dai duk da haka ta kara ne a matsayin ta biyu a rukunin D bayan zakarun na Jamus.

Bayern ce ta mamaye wasan da farko inda Thomas Muller ya fara cin kwallon sannan Mario Gotze ya kara ta biyu.

David Silva ne ya fara zarewa Manchester City kwallo daya kafin Aleksandar Kolarov ya mai da wasan kunnen doki ta hanyar bugun fenariti.

Daga bisani James Milner ya zura kwallon da ta bai wa City nasara.

Yanzu haka dai Bayern da City na da maki 15 sai dai Bayern tafi City adadin kwallaye a gasar, abinda ya sa ta zarra a rukunin.