Gerrard zai yi jinyar Raunin wata daya

Gerrard Injury
Image caption Dan wasan ya bugawa Liverpool jiga-jigan wasanni 15, ya kuma zura kwallaye uku a bana

Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard zai yi jinyar rauni na tsawon makwanni hudu, bayan da yaji rauni a karawar da suka casa West Ham da ci 4-1 a ranar Asabar.

An fidda Gerrard daga fili bayan an koma wasa zagaye na biyu a wasan da suka yi a Anfield, kuma zai yi jinyar ne tare da Daniel Sturridge wanda yake jinyar watanni biyu.

Dan wasan ya gamu da raunin ne lokacin da kocin kungiyar Brendan Rodgers zai yi matukar amfani da shi a fafatawar da za suyi da Tottenham da Manchester City da Chelsea a gasar Premier.

Liverpool tana matsayi na biyu a teburin Premier kuma ta baiwa Tottenham tazarar maki uku, ta kuma baiwa City tazarar maki guda, kuma yawan makinta daya da Chelsea amma tafi Chelsea da tazarar yawan zura kwallo.