Galatasaray ta doke Juventus 1-0

Galatasaray Juventus UEFA
Image caption Galatasaray ta sami kaiwa wasan kungiyoyi 16 a ci gaba da kofin zakarun Turai

Galatasaray ta doke Juventus da ci daya mai ban haushi a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai, a wasan da aka kammala a yau, bayan da jiya dusar kankara ta hana karasa wasan.

Wesley Sneijder ne ya zura kwallon da ya baiwa kungiyar damar kaiwa rukunin kungiyoyi 16 da za su rage a gasar; tuni Real Madrid ta jagoranci rukunin da Galatasaray ta kare a matsayi na biyu.

Kafin su kara dai Juventus na neman maki daya ne kacal wanda zai bata damar kaiwa zagayen wasan gaba, ganin kwarin gwiwar da take da shi da ta buga wasanni bakwai kwallo ba ta shiga ragarta ba a gasar Italiya.

Tun farkon karawar da suka yi a jiya an tashi wasa babu ci kafin dusar kankara ta dinga sauka a filin har ta sa aka tashi a wasan.