United za ta iya lashe kofin Turai-Moyes

Moyes Van Persie
Image caption Moyes na fatan kungiyarsa ta lashe kofin Turai idan 'yan wasa sun kara kokari

Kocin Manchester United David Moyes ya ce kungiyarsa ta na daga cikin wadanda za su iya lashe kofin zakarun Turai, amma sai sun kara kaimi.

United mai rike da kofin zakarun Turai karo uku, na fama da koma baya a gasar Premier, sai dai ta jagoranci rukunin farko a gasar kofin zakarun Turai bayan da ta samu nasara a kan Shakhtar Donetsk da ci daya mai ban haushi a gida.

Moyes ya ce "sai mun kara kwazo, domin kungiya kamar Manchester United ya kamata ta dinga daukar kofuna."

Kocin dan Scotland da ya maye gurbin Sir Alex Ferguson wanda ya lashe kofin karo biyu ya kara da ce wa "yayin da kake buga gasar shi ne kake kara gogewa sannu a hankali.