An ci Arsenal amma ta kai bantenta

Image caption Arsenal ta kai mataki na biyu duk da kayen da Napoli ta yi mata.

Arsenal ta samu shiga matakin sili biyu kwale a gasar Zakarun Turai bayan da ta zama ta biyu a rukunin F duk da kayen da ta sha a hannun Napoli.

Wannan ne karo na 14 a jere da Arsenal ke kai wa mataki na biyu a gasar.

Gonzalo Higuain ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal kafin a bai wa dan wasanta Mikel Arteta jan kati.

Sai dai duk da kwallo ta biyun da Jose Callejon ya zura, nasarar 2-1 da Borussia Dortmund ta samu kan Marseille ta sa an fitar da Napoli daga gasar.

Dortmund, Arsenal da Napoli duk sun kare wasanninsu na rukuni ne da maki 12, amma Jamusawan sun ciri tuta saboda nasarar da suka yi kan Arsenal a baya.

Arsenal kuma ta doke Napoli zuwa matsayi na biyu saboda ta fi ta zura kwallaye a raga.