Barca ta zane Celtic 6-1

Image caption Neymar ne ya zura kwallaye uku a wasan.

Barcelona ta yi raga-raga da Celtic a gasar Zakarun Turai, inda aka tashi 6-1.

Gerard Pique ne ya fara zura sannin Pedro da Neymar suka kara kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Dan wasan Brazil Neymar, wanda aka siyo shi kan fam miliyan 49 daga Santos ya kara kwallaye biyu kafin cikar sa'a guda da take wasa.

Cristian Tello ne ya cika she ta shidan, yayinda Georgios Samaras na Celtic ya samu zare kwallo guda.

Wannan nasara ta kawo karshen fafatawar Celtic a gasar Zakarun Turai ta bana.