Za a sauya sunan Hull City

Hull City
Image caption Kungiyar za ta tuntubi magoya bayanta

Magoya bayan Hull City sunki amince wa da a sauya sunan kungiyar, sunyi kira ga hukumar kwallon kafa ta kare sunan kulob din da al'adunsa.

Ranar Laraba ne Assem Allam mai kungiyar ya turawa hukumar kwallon kafa bukatar canja sunan kungiyar zuwa Hull Tigers.

Sai dai magoya bayan kungiyar suna gabatar da kamfain cewa a bar sunan City har bayan rayuwarsu, kuma suna fata hukumar ba za ta canja sunan kungiyar ba.

Idan kungiya tana son sauya sunanta sai an nemi izini daga hukuma, wacce take da damar amincewa ko akasin haka.