Mourinho na son karawa da Drogba

Mourinho Drogba
Image caption Mourinho na son ganin Drogba ya sake taka leda a Stamford Bridge

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya na son kungiyarsa ta hadu da Galatasaray a karawar kungiyoyi 16 da suka rage a gasar zakarun Turai ranar Litinin domin fuskankar Didier Drogba.

Drogba ya bar Chelsea a shekarar 2012, bayan da ya kwashe shekaru takwas ya na bugawa kungiyar wasa, shekara guda kofin Jose Mourinho ya sake dawowa Stamford Bridge a karo na biyu.

Mourinho ya ce "Karawa da Galatasaray wasa ne mai wuyar sha'ani, amma ina son Didier yazo filinmu ya buga wasa domin yaji yadda nake ji a yanzu."

Baya ga Galatasaray, za a iya hada Chelsea da Leverkusen ko Zenit St Petersburg ko Olympiakos ko AC Milan.