Van Persie zai yi jinyar wata daya

Image caption Robin van Persie

Dan kwallon Manchester United Robin van Persie, zai yi jinyar wata guda saboda rauni a cinyarsa.

Dan Holland mai shekaru 30, ya ji rauni lokacin da ya dauko bugun kusurwa da United, inda suka doke Shakhtar Donetsk daci daya mai ban haushi.

United za ta buga wasanni takwas kafi ta hadu da Chelsea a ranar 19 ga watan Junairu.

Kocin kungiyar David Moyes ya ce "Sakamakonmu ya fi kyau idan Wayne Rooney yana tare da Robin".

Van Persie ya koma Old Trafford a kan fan miliyan 24 daga Arsenal a watan Agustan 2012.

Karin bayani