Swansea ta haye a gasar Europa

Kocin Swansea
Image caption Kocin Swansea Michael Laudrup

Swansea ta kai matakin sili biyu kwale a gasar Europa duk da kwallon da Marco Mathys na St Gallen ya jefa mata a raga.

An dai tashi wasa Swansea ba ta farke ba, amma kunne dokin 1-1 da Kuban Krasnodar ta yi da Valencia ya sa ta hawa matsayi na biyu a cikin rukunin.

A wasansu na baya dai Swansea ta doke St Gallen da 1-0 don haka ko kunnen doki ta samu za ta haye zuwa gaba.

Ita kuwa St Gallen ta riga ta bare tun bayan da ta sha kaye wurin Kuban ta Rasha.