Europa: Tottenham ta casa Anzhi 4 da 1

Roberto Soldado
Image caption Roberto Soldado

A karo na farko a zuwansa Tottenham, Roberto Soldado ya ci kwallaye uku a wasa daya, abinda ya tabbatar da nasarar Spurs din a rukuninsu na gasar Europa.

Dama dai kungiyar ce jagorar rukunin G tun kafin wasan da suka buga da Anzhi Makhachkala.

Baya ga kwallayen Soldado uku, Lewis Holtby ya kara guda sannan Ewerton Almeida Santos na Anzhi ya zare daya, abinda ya sa aka tashi wasa 4-1.

Ita ma dai Anzhi ta samu wucewa matakin gaba tun kafin wannan wasan bayan da ta yi nasara a wasanninta na baya.