Aguero zai yi jinyar wata guda

Sergio Aguero
Image caption Dan wasan zai yi jinyar mako hudu

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce dan wasan kungiyar Sergio Aguero zai yi jinyar wata daya sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.

Kocin Manuel Pellegrini, ya ce dan wasan kungiyar Sergio Aguero zai yi jinyar wata daya .

Dan wasan da ke jagaba wajen yawan zura kwallaye 19 a kungiyar, ya ji raunin ne a gwiwarsa lokacin da suka lallasa Arsenal da ci 6-3 a ranar Asabar.

Dan kwallon Argentina ya zura kwallaye 13 a gasar Premier, kuma shi ya fara zura kwallo a ragar Arsenal a karawar da suka yi kafin ya ji rauni.

An dai sauya shi ne mintuna kadan da dawowa wasan zagaye na biyu.

City za ta kara da Leicester City a gasar League Cup a wasan gab da na kusa da na karshe ranar Talata.