Europa: Tottenham da Dnipro

Juande Ramos'
Image caption Tsohon kocin Tottenham da ya daukarwa kungiyar League cup a 2008 amma aka sallame shi

Tottenham za ta fafata da Dnipro kungiyar da tsohon kocinta Juande Ramos yake horas wa a wasannin kungiyoyi 32 da suka rage na cin kofin Europa League.

Kungiyar Swansea za ta kara da Napoli ta Italiya, kungiyar da Rafael Benitez tsohon kocin Liverpool da Chelsea yake horas wa.

Idan Tottenham ta lashe Dnipro to za ta fuskanci PAOK ko Benfica a wasan kungiyoyi 16 da za su rage a gasar, itama Swansea za ta iya haduwa da Porto ko Eintracht Frankfurt idan ta lashe wasanta.

Sauran wasanni Juventus za ta fafata da Trabzonspor, Ajax da Salzburg sai wasan Lazio da Ludogorets a wasannin kungiyoyi 32 da suka rage a gasar.

Wasannin da za su kara gida da waje, za a fara wasannin farko ranar 20 ga watan Fabrairu, da kuma wasa na biyu ranar 27 ga watan Fabrairun badi.