Tottenham ta kori Andre Villas-Boas

Image caption Andre Villas-Boas ya ce ba shi ke da alhakin korar kansa ba

Kungiyar kwallon kafar Tottenham ta kori kocinta, Andre Villas-Boas, sakamakon dokewar da Liverpool ta yi musu da ci 5-0 a gida.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ''Mun amince cewa koci Andre Villas-Boas zai ajiye aikinsa''.

Dokewar dai ita ce mafi muni da aka yi wa kungiyar a gida cikin shekaru 16, lamarin da ya sa ta kasance ta bakwai a teburin gasar Premier.

An dauki Villas-Boas, mai shekaru 36 aiki a Tottenham ne a watan Yunin 2012.

Karin bayani