Zola yayi ritaya daga kocin Watford

Gianfranco Zola
Image caption kocin yayi ritaya ganin kungiyar bata taka rawar gani a bana

Gianfranco Zola yayi ritaya daga kocin kungiyar Watford wacce take buga gasar Championship, sakamakon rashin tabuka rawar gani a kakar wasan bana.

Kocin mai shekaru 47 ya fara horad da Watford a watan Yulin shekarar 2012 ya kuma jagoranci kungiyar a wasan cike gurbin shiga gasar Premier a inda yayi rashin nasara a hannun Crystal Palace da ci daya mai ban haushi.

Watford tayi rashin nasara a wasanni biyar data buga a gida kuma rabonta da ta lashe wasa tun a watan Oktoba.

Tun a ranar Asabar kocin ya ce zai sanar da makomarsa a kungiyar, bayan da Sheffield Wednesday ta doke su da ci daya mai ban Haushi, kuma kungiyar ta fado matsayi na 13 daga teburi, wanda tun a farko take matsayi na 5.