Kocin Cardiff ya ce ba zai yi ritaya ba

Malky Mackay
Image caption Kocin ya ce bai ga dalilin da zai bar kocin Cardiff ba

Kocin Cardiff City Malky Mackay ya ce ba zai yi ritaya daga kocin kungiyar ba, duk da mai kungiyar ya na fushi da shi.

Babban jami'in kungiyar Simon Lim ya dugun zuma ran magoya bayan kungiyar lokacin da ya ce kocin ya batawa mai kungiyar rai, sakamakwan fatan da yayi na sayan 'yan wasa uku a watan Janairu idan an bude kasuwar cinikayyayr 'yan wasa.

Mackay ya sanar wa da BBC ce wa "bazan yi ritaya daga aiki na ba, kuma na kadu da jin kalaman Simon Lim."

Kocin mai shekaru 41 dan kasar Scotland ya ce baiga dalilin da zai bar aiki sa ba, don mai kungiyar ya ce ba zai bashi kudin sayen 'yan wasa a watan Janairu ba.