'Yan wasan Eritrea 9 da koci sun tsere

Eritrea Players  Missing
Image caption 'Yan wasan sun saba tserewa da zarar sun tafi wasa waje

Yan kwallon Eritrea su tara da koci sun tsere a Kenya bayan kammala gasar kwallon kafa na kasashen dake yankin tsakiya da gabashin yankin Afrika.

Bayan da aka cire Eritrea a gasar ne 'yan wasan suka kama gaban su, a gasar da Kenya ta karbi bakunci ta kuma lashe kofin.

Sakatare Janar Nicholas Musonye ya sanar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa 'yan wasa da kocin sun yi batan dabo.

Wannan ba shine karon farko ba da yan wasan kasar ke guduwa da zarar sun fita waje wasanni.

Kimanin 'yan wasa 17 ne da likitansu suka nemi mafaka a Uganda a bara, bayan watanni 18 'yan wasan Eritrea 13 suka nemi mafaka a Tanzaniya, kuma a shekara ta 2009 sama da yan wasa dozen ne suka gudu a Kenya.