FA na cajin Wilshere da cin zarafi

Jack Wilshere
Image caption Dan wasan an bashi nan da Laraba ya kare kansa

Hukumar kwallon kafa na cajin dan wasa Arsenal Jack Wilshere a kan cin zarafin 'yan kallo da ya yi nuni da yatsan sa.

Dan wasan mai shekaru 21, an dauki hotonsa a kamara yana nunin cin zarafin 'yan kallo a lokacin da Manchester City ta caskara su da ci 6-3 ranar Asabar.

Lokacin da dan wasan ya aika ta laifin alkalan wasa ba su ganshi ba, amma an dauki hoton bidiyo sanda yake nunin batanci, kuma tsofaffin alkalan wasa uku da aka nada suka kalli bidiyon suka kuma tuhumi dan wasan.

Wilshare ya ci zarafin magoya bayan City da yatsansa a minti na 68 lokacin da yake nuna rashin amincewa da hukuncin alkalin wasa da ya baiwa City dukan falan daya a filin Ettihad

An taba samun dan kwallon Liverpool Luis Suarez da laifin cin zarafin 'yan kallo da yatsa a karawa da suka yi da Fulham, a inda hukumar ta dakatar da shi wasa daya da cin tarar fan 20,000 da kuma gargadin gyara hali a shekarar 2011.