Manchester City ta casa Leicester 1-3

Image caption Edin Dzeko

Sau biyu Edin Dzeko na zura kwallo a raga a wasan da Manchester City ta lallasa Leicester, ta kuma samu zuwa matakin daf da na karshe a gasar cin kofin Capital One.

Dan wasan baya Aleksandar Kolarov ne ya fara jefa kwallo kafin Dzeko ya zura kwallayen na sa biyu.

Minti 13 kafin kare wasa, Lloyd Dyer na Leicester ya saka kwallon hana rantsuwa.

Wannan kwallon ce karo daya tilo a wasan da Leicester ta tabuka wani abu.