Montano ya karyata shiga cinikin wasa

Cristian Montano
Image caption Dan wasa ya ce zai nemi dalilin da yasa aka kore shi

Cristian Montano ya ki amincewa da sa hannu a cinikin wasan kwallon kafa bayan da kungiyarsa Oldham ta kore shi ranar Litinin.

Dan wasan mai shekaru 22, yana daga cikin 'yan wasa shida da aka tuhuma kan cinikin wasa, aka kuma bada shi beli tun lokacin da mujallar Sun ta bankado labarin.

Tuni kungiyar ta dakatar da shi daga lokacin da aka fara zarginsa, sai dai dan wasan ya ce zai bi ba'asin dalilin da yasa kungiyar ta sallame shi.

Montano ya koma Oldham a watan Agustan shekarar 2012, ya kuma buga wasanni 48 a inda ya zura kwallaye 4 a raga.