"Lashe Chelsea zai kara mana kwazo"

Gus Poyet
Image caption Zamu iya casa kowa tunda muka lashe Chelsea

Kocin Sunderland Gus Poyet yana fatan casa Chelsea da kungiyarsa ta yi a gasar Capital One Cup, zai kara musu kaimi a gasar Premier.

Dan wasan kungiyar Ki Sung-Yueng ne ya zura kwallo ta biyu da ta baiwa kungiyar damar kaiwa wasan kusa dana karshe, su ka kuma yi waje da Chelsea dake matsayi na uku a gasar Premier.

Poyet ya ce "ina son sauya tunanin zakakuren 'yan wasan da muke da su , domin mu dinga lashe wasanni."

Ya kara da ce wa "idan har zaka iya lashe daya daga cikin fitattun kungiyoyin da ake ji dasu a kasar, to zaka iya casa sauran kungiyoyin dake buga gasar."

Tun lokacin da Poyet dan kasar Uruguay ya karbi Black Cats ranar 5 da watan Oktoba ya lashe wasanni hudu daga cikin wasanni 11 da ya kara.