Watford ta dauki koci Sannino

Giuseppe Sannino
Image caption Karon farko da kocin zai horas a Ingila

Kungiyar Warford mai buga gasar Championship ta bada sanarwar daukar sabon koci Giuseppe Sannino, sakamakon ritaya da tsohon kocin kungiyar Gianfranco Zola ya yi.

Sannino, mai shekaru 56, bai taba koci in ba a cikin Italiya ba, kuma Watford itace kungiya ta 13 da kocin zai jagoranta, cikin kungiyoyin da ya horas har da Siena da Palermo da Chievo Verona.

Kocin dan kasar Italiya zai yi aiki tare da mataimaka da suka hada da Francesco Troise da Giovanni Cusatis da Paolo De Toffol, kuma Watford tana matsayi na 13 a teburin gasar Championship.

Kafin Zola ya yi ritaya ranar Litinin, kungiyar ta buga wasanni 10 ta samu nasara a wasa daya kacal, har da rashin nasarar wasannin biyar a jere da kungiyar ta yi wasa a gidanta.