FA ta dakatar da Wilshere wasanni 2

Jack Wilshere
Image caption An dakatar da dan wasan wasanni biyu

Hukumar kwallon kafar Ingila ta dakatar da dan kwallon Arsenal, Jack Wilshere, daga buga wasanni biyu bayan ta same shi da laifin cin zarafin 'yan kallo da yatsansa.

Dan wasan mai shekaru 21, ya amince da tuhumar da aka yi masa, amma ya daukaka kara a kan dakatar da shi wasanni biyu.

Kwamitin ladabtarwa mai zaman kansa ne ya ki amincewa da daukaka karar da dan wasan ya shigar aka kuma saurara ranar Alhamis.

An dauki hoton bidiyon dan wasan lokacin da yake cin zarafin magoya bayan Manchester City a karawar da aka casa su da ci 6-3 a Ettihad.

Hukumar FA, ta sanar da cewa dan wasan ya amince da laifin da ya aikata, amma ya kalubalanci hukuncin dakatarwar wasanni biyu, a inda aka tabbatar masa da hukuncin da ya fara aiki nan take na hutun wasanni biyu.

Dan wasan ba zai buga karawar da Arsenal za ta yi da Chelsea ba a ranar Litinin da kuma karawa da za su yi da West Ham.