Raja Casablanca ta casa Mineiro 3-1

Image caption Mouhssine Moutaouali na Raja Casablanca na murnar samun zuwa wasan karshe na gasar zakarun duniya.

Raja Casablanca ta ci kwallaye biyu a mintuna 10 na karshe a wasan da ta lallasa Atletico Mineiro ta Brazil a matakin kusa da na karshe na gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa ta duniya, inda za ta buga da Bayern Munich a wasan karshe.

Raja ce ta fara zura kwallo bayan hutun rabin lokaci inda dan wasanta Mouhssine Iajour ya ci daga nesa.

Tsohon dan wasan Barcelona da AC Milan Ronaldinho ne ya farkewa Atletico Mineiro lokacin da ya yi bugun tazara.

A minti na 83 Mohaine Moutaouali na Raja ya ci da fenariti bayan da alkali ya ce Rever ya kada Iajour, duk da hukuncin ya haddasa kace-nace.

A cikin minti hudu na karin lokaci Vivien Mabide ya zare shakku inda ya tamfatsa wata kwallon a ragar Mineiro.

Yanzu haka dai Raja za ta kara da zakarun Turai ne Bayern Munich a ranar Asabar a Marrakesh.

Wannan shi ne karo na biyu tun fara gasar a 2005 da ba za'a buga wasan karshe tsakanin kungiyoyin Turai da Amurka ta Kudu ba.