Ba ji idan Laudrup zai bar mu -Swansea

Michael Laudrup
Image caption Kocin ya sha fada cewar yana jin dadin zama a Swansea

Kungiyar Swansea ta ce ba za ta damu ba idan kocinta, Michael Laudrup, zai bar ta ya koma Tottenham.

Laudrup yana daga cikin kociyoyin da ake hasashen za su gaji Andre Villas-Boas, wanda Spurs ta sallama ranar Litinin bayan kungiyar ta sha kashi a hannun Liverpool da ci 5-0.

Morten Wieghorst, mataimakin kocin Swansea, ya ce "bana jin kungiyarmu za ta damu da rade radin da ake yi cewa zai barmu, domin an sha danganta shi yunkurin barinmu, amma yakan ce yana jin dadin zama da mu."

Sai dai ya kara da cewa "ba zan ga laifinsa ba idan ya koma wata mashahuriyar kungiyar."