Messi ya soma murmurewa

Image caption Lionel Messi

Dan kwallon Barcelona, Lionel Messi ya soma murmurewa daga raunin da ya ke fama dashi a kafarsa.

Dan wasan na Argentina wanda a yanzu haka yake Buenos Aires inda yake jinya, na samun sauki.

Likitan 'yan wasan Barcelona Richard Pruno, ya ce dan kwallon mai shekaru 26 na samun sauki.

Raunin ya sa zai yi jinyar makwanni shida zuwa takwas wato sai watan Junairu zai koma taka leda.

Messi ya ji rauni ne a ranar 10 ga watan Nuwamba a wasansu da Real Betis.

Karin bayani