Bayern Munich ta dauki Kofin Duniya

Image caption Wannan shi ne karon farko da wata kungiyar Jamus ta sami zuwa gasar.

Bayern Munich ta dauki kofin zakarun nahiyoyi na duniya bayan da ta ci Raja Casablanca ta Morocco da ci 2-0.

Dante ne ya fara zura kwallo ragar kungiyar ta Morocco minti bakwai da fara wasa.

A minti na 22 ne kuma sai Thiago Alcantara ya jefa ta biyu.

Wannan shi ne karon farko da wata kungiyar Jamus ta sami zuwa gasar.

Da wannan nasara kociyan Bayern Munich Pep Guardiola ya zama na farko da ya dauki kofin sau uku.

A baya kociyan ya dauka sau biyu da Barcelona.

Kungiyar ta Jamus ta kara wannan kofin ne akan na Zakarun Turai da na gasar lig din Jamus da kofin kalubale na Jamus da kuma kofin zakaru na Uefa(super cup)

An yi wasan ne a birnin Marrakech na kasar ta Morocco.