Kofin Premier na City ne in ji Rodgers

brendan rodger
Image caption Sai Manchester City sun barar da damar su, sannan mu lashe kofin Premier bana

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce Manchester City ce za ta lashe kofin Premier na bana, duk da kungiyarsa ta dare matsayi na daya a teburi, bayan da ta casa Cardiff da ci 3-1 ranar Asabar.

Liverpool ta bai wa City tazarar maki daya, kafin su kara ranar Alhamis a filin wasa na Ettihad, sai dai Arsenal za ta iya komawa matsayinta na daya idan ta doke Chelsea a ranar Litinin.

Rodger ya ce "idan za mu dauki kofin Premier bana, sai in Manchester City sun gaza, domin suna da hazikan 'yan wasa kuma sun tara gogaggun 'yan kwallo."

Arsenal na bukatar doke Chelsea ranar Litinin kafin ta koma matsayinta na daya a teburi, idan kuwa Chelsea ce ta doke Arsenal to za ta hada maki daidai da Liverpool, sai dai Liverpool tana da yawan tazarar kwallaye a raga.

Idan kuwa Liverpool ta jagoranci teburin Premier har Kirsimeti, zai zama karon farko da ta hau matsayin wanda rabonta da shi tun a shekara ta 2009, kuma rabon ta dare teburi a Kirsimeti ta kuma lashe kofin tun a shekarar kakar wasanni ta 1987-88.