Lokaci na kurewa Sunderland — Poyet

Gus Poyet
Image caption A kwai jan aiki kofin mu tsira daga fadowa daga Premier

Kocin Sunderland Gus Poyet ya ce lokaci sai kara kurewa kungiyar yake yi, a kokarin da take na kaucewa fadowa daga gasar Premier a kakar bana.

Sunderland tana matsayi na karshe a teburi ya yin da gasar za ta kai Kirsimeti, kuma West Brom ce kadai ta taba kaucewa fadowa daga Premier a yanayi irin wannan a shekarar 2004-05.

Poyet ya ce "lokaci yana kure mana, kuma muna kara rashin nasara a wasanni, muna bukatar lashe wasanni 11 nan gaba, ko kuma mu sami maki 40 wanda abin da wuya."

Sunderland ta doke Chelsea a Capital Cup a wasan daf da na kusa da karshe, amma ta tashi wasa babu ci da Norwich a gasar Premier da ta buga ranar Asabar.