Aboutrika ya yi ritaya daga kwallon kafa

Mohamed Aboutrika
Image caption Dan wasan bai taba halartar gasar kofin duniya ba

Kungiyar Al Ahly ta tabbatar da cewa Mohamed Aboutrika ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.

Dan wasan mai shekaru 35, mai buga tsakiya ya sanar da zai yi ritaya tun lokacin da kungiyarsa ta kasa haura gasar cin kofin duniya a wasan daf da na kusa da karshe a Morocco, kuma kungiyar ta kasa rarrashin dan wasa kar ya yi ritaya.

Wasan karshe da dan wasan ya buga shine karawar da su ka yi da Guangzhou ranar 14 Disamba, bayan da suka yi rashin nasara a wasan da ci biyu da nema, aka kuma canja Aboutrika bayan an dawo wasan zagaye na biyu lokacin da ya fadi a fili.

Dan wasan bai sami bugawa kungiyarsa wasan neman matsayi na uku ba, a gasar cin kofin duniya ta zakarun nahiyoyi.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Khaled Mortagy ya shaida wa BBC ce wa "Aboutrika dan wasa ne abin koyi kuma ritayarsa hasara ce ga wasan kwallon kafa a Masar."

Aboutrika, ya bugawa Masar wasanni sama da 100 ya lashe kofin nahiyar Afrika sau biyu a shekarun 2006 da 2008, bai sami halartar gasar shekara ta 2010 ba wanda Masar ta lashe kofin sakamakon rauni da ya yi jinya.

Ya zura kwallaye 14 a kokarin da Masar ta yi na neman gurbin shiga kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci a badi, ko da yake Masar ba ta sami gurbin zuwa gasar ba.