Spurs ba ta mutuntani ba - Adebayor

Image caption Emmanuel Adebayor

Dan kwallon Togo, Emmanuel Adebayor ya zargi kungiyar Tottenham da cewar ba ta mutuntashi ba.

Ya ci kwallaye biyu a wasan da aka soma dashi a karon farko a kakar wasa ta bana, inda Spurs ta doke Southampton daci uku da biyu a ranar Lahadi.

Dan kwallo mai shekaru 29, ba ya cikin hoton 'yan wasan kulob din, sannan kuma kocin da aka kora Andre Villas-Boas ya sa shi ya dunga horo shi kadai.

Adebayor yace "Abin nada wuya, idan na zo horo naga hoton da bana ciki, hakan na nuna rashin mutunta ni."

Dan wasan ya koma Tottenham ne daga Manchester City a shekara ta 2012 a kan fan miliyan biyar.

Karin bayani