An yi wa Fellaini aiki a kugu

Marouane Fellaini
Image caption Dan wasan zai ci gaba da jinyar rauni

Dan wasan Manchester United Marouane Fellaini zai ci gaba da jinya, bayan da likitoci suka yi masa aiki a kugunsa.

Dan wasan mai shekaru 26, tsohon dan kwallon Everton ya yi fama da raunin ciwon baya, wanda sai canja shi aka yi a karawar da Everton ta doke United ranar 4 ga watan Disamba.

United sai da ta jira sakamakon gwajin da likitoci suka yi masa, kafin ta amince a yiwa dan wasan tiyata.

Fellaini ya gamu da raunin ne a karawar da United ta yi da Shakhtar Donetsk a gasar kofin zakarun Turai a wasannin cikin rukuni a watan Oktoba.