Super Eagles za ta kara da Kano Pillars

stephen keshi
Image caption Super Eagles na fatan lashe kofin a karon farko

Tawagar Super Eagles ta Nigeria za ta buga wasan sada zumunci da kungiyar Kano Pillars a wasan sada zumunci a ranar.

Wasan na daga cikin shirye-shiryen Super Eagles din don tunkarar gasar kofin nahiyar Afirka ta 'yan kwallon dake taka leda a cikin gida.

Za a buga wasan sada zumunci a katafaren filin wasa na kasa da ke Abuja.

Haka kuma Super Eagles din ta gayyaci golan Taraba United United Ibrahim Pius zuwa sansanin horanta.

Golan zai fafata wajen gurbin dan wasan da zai kamawa Najeriya kwallo a raga tare da Chigozie Agbim da Daniel Akpeyi da golan matasa yan kasa da shekaru 17 Dele Alampasu da tuni suna sansanin horon.

Cikin wasannin sada zumunci da Super Eagles ta buga a baya baya nan, ta casa sabuwar kungiyar da ta hauro gasar Premier wato Prisons FC ta Abuja da ci 4-1, ta kuma casa Niger Tornadoes ta Minna da Plateau United da ci biyu ba ko daya kowannensu.

Mataimakin kocin kungiyar Daniel Amokachi, ya ce za a ci gaba da gayyato sabbin yan wasa da kuma gwada su, da nufin zabar zakakuren 'yan wasan da zasu taka rawar gani da Nijeriya za tayi alfahari da su.