'Akwai mamaki a gasar Premier ta bana'

Image caption Manyan kungiyoyin a gasar Premier ta Ingila

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce gasar premier ta bana na cike da abin mamaki saboda ana tafiya ne kusan kunnen doki saboda maki biyu ne kawai ya raba tsakanin kungiyoyin biyar na farko.

Bayan an tashi babu ci tsakanin Arsenal da Chelsea, yanzu dai Arsenal ce ta biyu inda yawan kwallaye ne suka raba tsakaninta da Liverpool a yayinda Chelsea ke matakin na hudu.

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewar "Abin na da ban sha'awa saboda manyan kungiyoyin na tafiya a tare".

A washe garin kirismeti ne za a koma fafatawa a gasar Premiet ta Ingila.

Karin bayani