Sherwood ya tabbata kocin Tottenham

Image caption Tim Sherwood ya maye gurbin Andre Villas-Boas.

Tottenham ta nada Tim Sherwood a matsayin cikakken kocinta.

Tsohon dan wasan tsakiyar na Ingila ne ya jagoranci Spurs din a nasarar 3-2 da ta samu kan Southampton ranar Lahadi a matsayin kocin wucin gadi, amma yanzu an tabbatar masa da mukamin har zuwa karshen kakar wasannin Premier ta 2014-2015.

Sherwood mai shekaru 44 ya maye gurbin Andre Villas-Boas ne wanda Spurs ta kora makon jiya.

Sabon kocin ya zama dan wasan Tottenham ne a 1999 daga Blackburn, inda ya daga kofin Premier a 1995.

A 2003 ya koma Portsmouth sannan ya shiga sahun masu horar da 'yan wasan kungiyar a 2008 karkashin Harry Redknapp.