Masoyan Cardiff na iya adawa - Mackay

Image caption Vincent Tan ya so korar Mackay amma ya fasa

Kocin Cardiff Malky Mackay ya ce magoya bayan kungiyar na da hakkin nuna adawarsu game da takaddamarsa da mai kungiyar Vincent Tan.

A makon jiya ne Tan ya ce da Mackay ya ajiye aiki ko ya kore shi.

Tuni dai ya janye barazanar kuma shugaban kungiyar Mehmet Dalman ya roki magoya bayan da aka su nuna adawa da Tan a wasan da kungiyar za ta buga da Southampton washe garin Kirismeti.

Sai dai Mackay ya ce idan magoya baya sun nuna rashin amincewa da abinda aka yi masa ba su yi lafi ba.