Liverpool za ta fid da raini da Man City

Luis Suarez
Image caption Liverpool ce jagaba a rukunin Premier

Liverpool ce jagorar rukunin Premier a yanzu, amma ziyarar da za ta kai Manchester City ranar Alhamis ita ce 'yar manuniyar ko za ta iya dorewa.

Maki daya ne tsakanin Liverpool da City da ke mataki na uku, wacce ba ta fadi wasa ko daya a filinta na Etihad a kakar bana ba.

Tazarar maki biyu ce kacal ta raba kungiyoyi biyar da ke saman rukunin.

Arsenal, ta biyu za ta kara da West Ham, yayin da Chelsea, ta hudu, za ta karbi bakuncin Swansea. Everton, ta biyar, na karbar bakuncin Sunderland, inda Manchester United za ta je Hull.

United mai rike da kambu na mataki na takwas, da tazarar maki takwas tsakaninta da Liverpool.