Man U ta sha da kyar a Hull City

Wayne Rooney
Image caption Wayne Rooney yaci kwallo 150 a gasar Premier

Kwallon da James Chester na Hull ya ci gida ta bai wa Manchester United nasara a wasan da suka tashi 2-3.

Chester na ya zura kwallon farko kafin David Meyler ya kara ta biyu bayan mintinu 12.

Sai dai Chris Smalling na United ya farke daya da ka kafin Wayne Rooney ya tamfatsa ta biyu daga tsakiyar fili, kwallo ta 150 ke nan da ci wa United a gasar Premier.

Tsohon dan United Chester ya ci gida ne bayan hutun rabin lokaci, inda daga bisani kuma aka bai wa Antonio Valencia na United jan kati.