Arsenal ta koma matsayinta a Premier

Image caption Lukas Podolski da Theo Walcott sun mayar da Arsenal matsayinta na jagorar gasar Premier.

Theo Walcott ya zura kwallaye biyu yayin da Podolski ya kara ta uku a wasan da Arsenal ta lallasa West Ham 3-1 ta kuma dawo kan matsayinta na jagorar rukunin Premier.

Arsenal ce ta mamaye rabin lokaci na farko amma West Ham ta yi mata zarra sakamakon kwallon Carlton Cole.

West Ham ta barar da damarta kafin Walcott ya farke da kwallon da ya kamata a ce gola ya kare.

Podolski ya gara wa Walcott ya zura ta biyu kafin shi da kansa ya kara ta ukun.

Sakamakon sauran wasanni sun sa West Ham ta fada mataki na 19 cikin masu shirin sauka daga rukunin Premier.